Labarai
Arewa na da kwararrun da za su magance matsalolin yankin- Uba Sani

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa, yankin Arewacin Nijeriya na da kwararru da hazikan Mutane da za su iya magance matsalolin rashin ci gaba da ake fama da su, muddin manyan yankin suka haɗa kai domin tafiyar hanya ɗaya.
Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da shugabancin Arewa Consultative Forum ACF, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bashir Dalhatu, ya kai masa ziyara a Kaduna.
Ya ce lokaci ya yi da Arewa za ta tashi tsaye don ta yi aiki wajen warware talauci, gibin ilimi da matsalolin lafiya da suka daɗe suna damun yankin.
Gwamnan ya jaddada cewa Arewa na da dubban kwararru a fannonin kasuwanci, harkokin lafiya, masana’antu, karatu da kirkire-kirkire, waɗanda ake buƙatar haɗa su a wuri ɗaya.
You must be logged in to post a comment Login