Labaran Kano
Asalin cutar Tamowa na afkuwa ne tun kafin a haifi jariri- Likita
Shugabar Sashin kula da ingancin abinci mai gina jiki a ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Hajiya Halima Musa Yakasai, ta ce jihar Kano ce tafi kowacce jiha a fadin kasar nan yawan yaran da a ke haihuwa da cutar Tamowa.
Yayin da gwamnatin ke yin kokari wajan kare lafiyar kananan yara tare da kuma dakile matsalar cutar ta Tamowa.
Hajiya Halima Musa ta bayyana hakan ne yayin da a ke tattaunawa da ita a cikin shirin Duniyar Mu A Yau na nan gidan freedom Rediyo da ya maida hakalin kan karancin abinci mai gina jiki da a ke fama dashi a kasar nan.
Ta kuma ce, idan ana maganar abinci mai gina jiki bawai sai nau’in kayan abinci masu tsada ba, akwai kayayyakin abinci masu gina jiki kamar su Dawa da Gero da kwai da Wake da gujiya da kuma gyada.
A na sa bangaran, likitan kananan yara a asibitin koyar na malam Aminu dake nan Kano, Dakta Muhammad Kabir Abdullahi, ya ce karancin abinci mai gina jiki musamman ma ga kananan yara shine ke haifar da cutar ta Tamowa wadda babbar barazanace ga lafiya yara.
Ya bayyana cewa cutar Tamowa na samo asaline tun kafin a haifi yaro sakamakon rashin ingantaccen abinci a jikin mace mai juna biyu shine ke sa a haifi yara masu dauke da cutar.
Ya kara da cewa, yara da ke dauke da cutar ta Tamowa kaiya warkewa daga cutar matukar za su iya samun shayarwa daga iyayen su na tsaron watanin shidda kafin a fara hada musu da nau’in abinci masu gina jiki.
Hukumomin kiwon lafiya na yin dukkanin mai yuwa kan cutar lassa- Sarkin Kano
Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano
Ya ce, alamomin cutar Tamowa na fara nunawa a jikin yaro ta hanyar rashin ingantaccen abinci a cikin jikin yaro sai kaga fatar jikin yaro na yin yaushi, yana yawan kuka a koda yaushe da kuma rashin san wani ya matso kusa dashi sai kuma kaga yaro yana ramewa.
Sai kuma jami’in gamayyar kungiyoyin rajin yaki da karancin ingantaccen abinci mai gina jiki ta kasa, Ahmed Tijjani Ya’u, ya bayyana cewa gamayyar kungiyoyin na kokarin wayar da kan al’umma kan muhimmacin amfani da abinci mai gina jiki musamman ga kananan yara tareda bayar da tallafin nau’ikan abincin masu gina jiki don magance matsalar cutar yunwa a fadin jihar nan.