Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kungiyar Save the children da Action against hunger sun kaddamar da Shirin tallafawa al’umma a jihohin Kano da Kaduna.

Published

on

Kungiyar Save the children da hadin gwiwar masu yaki da cutar yunwa wato Action against hunger sun kaddamar da Shirin taimakawa kananan yara domin yaki da rashin isasshen abinci a jihohin Kano da Kaduna.
Da take jawabi lokacin kaddamar da Shirin shugabar Shirin KARINA LOPEZ tace Shirin na Kano da Kaduna ya biyo bayan nasarori da Shirin ya samu a jihohin Jigawa da Zamfara.
shirin na nufin dubawa da taimakon yara a kwanakin su dubu na farko daga lokacin da aka haife su.
Karina Lopez ta Kara da cewa ta hanyar bibiya zaa samu nasarar yaki da cutar tamowa tsakanin kananan yara ta hanyar bayar da tallafi mai karfi a tsakanin iyalai  dake fuskantar matsanancin talauci.
A nasa jawabin babban sakatare a maaikatar lafiya ta jahar Kano Alhaji Usman Bala Muhammad yace maganin cutar yunwa tsakanin kananan yara zai taimaka gaya wajen girman su.
Yace Gwamnatin Jahar Kano a shirye take wajen ganin ta taimaki Shirin wajen bayar da nata tallafin domin shiga loko da sako na jahar Kano.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!