Kasuwanci
Asusun ajiyar kuɗaɗen ƙetare na Najeriya ya sauka bayan da ya kai dala biliyan 33.59
Asusun ajiyar kudaden ketare a Najeriya ya sake faɗuwa bayan da ya tashi zuwa dala biliyan 33.59, mafi girma sama da wata daya.
A wata sanarwa da babban Bankin ƙasa ya fitar, asusun wanda ya faɗi ƙasa da dala biliyan 33.09 a ranar 12 ga watan Yuli, ya sami tagomashin dala miliyan 500 a kusan wata guda, ya kuma tsaya kan dala biliyan 33.59 a ranar 10 ga Agusta.
Haka zalika asusun ya sauka zuwa dala biliyan 33.58 a ranar 12 ga watan Augusta.
A wata sanarwar da ke da alaƙa, ta ce jimillar hada-hadar kasuwancin da aka gudanar kan farashin FMDQ ya tashi da kusan kashi 2.24 cikin ɗari a makon da ya gabata.
Jimilar ribar kuɗaɗen da aka samu a karshen makon da ya gabata 13 ga watan Augusta sun kai dala miliyan 692.60 sama da dala miliyan 677.44 da aka samu a wancan makon.
You must be logged in to post a comment Login