Connect with us

Labarai

Atiku ya zargi Gwamnatin Tinubu da kassara jam’iyyun adawa

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike, da amfani da karfin gwamnati wajen kassara jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027.

Atiku ya yi wannan zargin ne bayan da aka hana PDP amfani da wani wurin taro a Abuja domin gudanar da taron tabbatar da dan takararta na shugaban kasa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya bayyana matakin a matsayin wanda ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa tare da nuna wariyar siyasa.

Ya ce hana jam’iyya mai rajista gudanar da taro cikin lumana ya saba wa dimokradiyya da Kuma abunda da doka ta tanada.

Ya kuma zargi gwamnatin APC da kokarin rage tasirin jam’iyyun adawa ta hanyar amfani da cibiyoyin gwamnati domin hana su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!