Labarai
Atiku Abubakar:Babbar kotun Abuja ta ja kunnen shugaba Buhari da jami’an tsaro ga lamuran zabukan kasa
Dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci babbar kotun birnin tarayya Abuja da ta ja kunnen shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an tsaro daga tsunduma bakin su a lamuran babban zabukan kasa da za ayi.
Haka zalika Atiku Abubakar ya kuma ce kotun, ta tursasa shugaba Buhari ya biya shi diyyar naira biliyan biyu sannan ya bashi hakuri sakamakon daukar nauyin abin da ya kira gurfanar da shi kotu ba tare da ya aikata laifin komai ba.
Hakan na cikin takardar karar a matsayin mai da martini ga karar da kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari ya shigar gaban kotu wanda ya bukaci kotu ta tursasa Atiku ya biya shugaba Buhari diyyar naira miliyan arba’in saboda cin zarafin shugaba Buhari da iyalansa da shi Atikun ya yi.
Tun farko dai kwamitin yakin neman zaben shugaba Buhari ya gurfanar da Atiku Abubakar da mai Magana da yawunsa Phrank Shuaibu sakamakon bata sunan shugaba Buhari da iyalansa na cewa sun mallaki hannayen jari a daya daga cikin manyan bankunan kasuwancin kasar nan da kuma daya daga cikin kamfanin sadarwa.
Lamarin da ya sa Atiku Abubakar ta bakin lauyan sa Mr Chukwuma-Machukwu Ume ya kalubalanci karar yana mai zargin shugaba Buhari da bata sunan Atiku kan laifin da bashi ya aikata ba.