Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ci gaba da tsare mu bayan Buhari ya yi mana afuwa – Sojoji

Published

on

Sojojin nan sittin da shida wadanda wata kotun soji ta kamasu da laifi a kwanakin baya kafin daga bisani shugaba Buhari ya yi musu afuwa, sun shigar da kara gaban babbar kotun tarayya da ke Lagos, suna kalubalantar ci gaba da tsaresu a gidan gyaran hali.

Sojojin sun kuma bukaci kotun ta tursasa ministan cikin gida Rauf Aregbesola da shugaban hukumar kula da gyaran hali ta kasa, Ja’afaru Ahmed da su biya su diyyar naira biliyan daya da miliyan dari uku da ashirin sakamakon danne musu ‘yancinsu na walwala.

Lauyan sojojin Funmi Falana SAN, ta ce ci gaba da tsare wadanda ta ke karewar a gidan gyaran halin duk da cewa shugaba Buhari yayi musu afuwa tun a ranar tara ga watan Afrilun bana, ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan.

Saboda haka ta bukaci kotun da ta tursasa wadanda suke da hannu wajen ci gaba da tsaresu a gidan gyaran halin da su biya su diyya.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!