Connect with us

Labarai

Atiku ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin da Kotun Koli

Published

on

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin da Kotun Kolin kasar nan ta yanke dangane da rikicin shugabancin Jam’iyyar ADC.

 

Atiku ya bayyana hukuncin a matsayin wata nasara ga dimokuraɗiyya da kuma al’ummar Najeriya baki ɗaya, yana mai cewa wannan mataki ya nuna cewa tsarin shari’a na ƙasar nan na aiki yadda ya kamata.

 

Sai dai duk da haka, ya jaddada cewa har yanzu tafiyar ba ta ƙare ba, domin a cewarsa, akwai sauran aiki mai yawa wajen tabbatar da adalci da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

 

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci mambobin jam’iyyar da magoya bayanta da su ci gaba da jajircewa da gwagwarmaya domin ganin an samu cikakken daidaito da ci gaba a harkokin siyasa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!