Connect with us

Labarai

Muna daf da kawo ƙarshen yajin aikin ma’aikatan shari’a- Gwamnatin Abia

Published

on

Gwamnatin Jihar Abia, ta bayyana cewa ana daf da kawo ƙarshen yajin aikin da ƙungiyar ma’aikatan shari’a ta Judicial Staff Union of Nigeria ke yi, bayan samun gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi tsakanin ɓangarorin biyu.

 

A cewar gwamnati, an samu daidaito kan muhimman batutuwa da suka haɗa da biyan alawus-alawus na hutu da kuma batun fansho, wanda ya daɗe yana ɗaya daga cikin manyan dalilan da suka haddasa yajin aikin.

 

Sai dai gwamnatin ta soki matsayin da kungiyar lauyoyin ta ɗauka kan lamarin, inda ta ce wasu daga cikin kalaman ƙungiyar ba su taimaka wajen warware matsalar ba, illa ma ƙara dagula al’amura.

 

Gwamnatin jihar ta kuma jaddada kudirinta na ci gaba da tattaunawa da JUSUN domin ganin an kawo ƙarshen yajin aikin gaba ɗaya, tare da dawo da ayyukan kotuna yadda ya kamata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!