Labarai
Shugaba Tinubu ya miƙa sunan Joseph Tegbe domin nada Ministan Lantarki

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa sunan Joseph Olasunkanmi Tegbe domin zama sabon Ministan Wutar Lantarki.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis, inda ya ce an tura sunan Tegbe zuwa Majalisar Dattawa domin tantancewa da amincewa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.
Sanarwar ta ƙara da cewa, wannan naɗi na jiran sahalewar Majalisar Dattawa kafin ya zama cikakke ministan.
Shirin na naɗin Joseph Olasunkanmi Tegbe, dai ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, wanda ya ajiye muƙaminsa domin mayar da hankali kan takarar gwamna a Jihar Oyo gabanin zaɓen shekarar 2027.
You must be logged in to post a comment Login