Labaran Wasanni
Ayi wasa ban zura kwallo a raga ba shine ya fi batamin rai- Abdull Attacker
Wani matashi a nan Kano Abdulmajid Aminu Wanda akafi sani da (Abdul attacker) ya bayyana gaza zura kwallo yayin fafata wasa shi ne abin da ya ke bata masa rai.
Abdul attacker dan shekara 18 wanda dan asalin jihar Kano ne ya salon da yake taka Leda dai na kama da irin na fitattun ‘yan Kwallon kafa a Duniya.
Matashin dan wasan dai zuwa yanzu ya samu nasarar zura kwallaye 78, a raga cikin shekaru kalilan dayayi Yana taka leda a kungiyoyin Golden Bullet da Kuma Dabo Bebies dukkan su a jihar Kano.
Cikin kungiyoyin da Abdul ya zurawa kwallaye harda Kano Pillars, wadda ya zura mata kwallo uku a raga lamarin da ya sa tawagar gayyatar sa wasannin share fagen wato (pree season matches).
Inda ya samu nasarar zura kwallo guda a raga a wasanni biyun da ya bugawa Kano Pillars.
Zuwa yanzu dai dan wasa Abdull na fafata wasa a cibiyar horas da yan wasa ta Yaks sports limited dake jihar Lagos karkashin tsohon zakaran kwallon kafar Najeriya Yakubu Ayegbeni.
“Nafi sha’awar jefa kwallo ta kusurwar raga ko kuma na ratsa masu tsaron baya a guje kafin jefa kwallo, kuma ni ‘yan wasa Zlatan Ibrahimovic da kuma wayney Rooney har da Kareem Banzema sune nake kwaikwayo da su” a cewar Abdul Aminu.
A gefe guda du bada cewa iyayen Abdul masu karamin karfi ne, amma hakan bai hanasu bashi kwarin gwiwar tabbatuwar mafarkin sa ba.
Inda dan wasan ya samu gudunmawar fitaccen dan jaridar nan na wato Abubakar Isah Dandago Wanda ya zame masa jagoran bashi shawarwari da karfafa gwiwa.
You must be logged in to post a comment Login