Labarai
Ayyukan raya kasa : Buhari zai cigaba da shinfida tituna a Najeriya

Hukumar gyaran titina ta Kasa (FERMA) ta ce zata ci gaba da shinfida sababbin tituna tare da gyaran titinan da suka lalace a fadin Kasar nan.
Shugaban Hukumar ta kasa reshen Jihar Kano, Injiniya Sani Abdulkadir ne ya bayyana hakan, lokacin da kwamitin Majalisar wakilai ke duba irin ayyukan da hukumar ke gudanarwa a Jihar Kano.
Injiniya Sani Abdulkadir ya ce hukumar ta gyara tinina da dama a nan jihar Kano da suka hadar da titin Wudil da Gaya da kuma Titin Danbatta da Hotoro da ma wasu da dama.
You must be logged in to post a comment Login