Labaran Kano
Azabtarwa: Almajiri ya rasa hanayen sa a Kano
Wani malami ya azabtar da dalibinsa karamin yaro, wanda har ta kai ya nakasa a hannu, a karamar hukumar Sumaila dake nan Kano.
Ana zargin malamin tsangayar dake karamar hukumar Sumaila na aika almajiransa bara don su kawo masa harajin naira 40 kowacce rana.
Sakamakon rashin kawo harajin na naira 40 ne, ya sanya malamin ya azabtar da shi, wadda har ta yi sanadiyar rubewar hannayen sa.
Tun farkon faruwar abin ne kwamishinan shari’a na jihar jigawa Barista Musa Adamu Aliyu ya shiga maganar domin tabbatar da ganin an yi adalci.
To amma ga alama akwai iyakarsa akan wannan yunkurin duk da cewa yaron dan Birnin Kudu ne a jihar jigawa amma abin ya faru ne a Sumaila dake nan Kano don haka dole mahukuntan Kano ne zasu dauki mataki.
Wata wasika da mahukuntan jihar Jigawan suka aikawa babban mai shari’a na nan Kano ta neme shi da ya dauki matakan gurfanar da wannan alaramma a kotu domin ya girbe abin da ya shuka, musamman la’akari da yadda hannuwan wannan yaro suka lalace.
Zuwa yanzu dai kungiyar mata lauyoyi ta duniya reshen jihar Kano, ta shiga wannan magana har ma ta nemi kwamishinan’yan sandan jihar Kano da ya kamo alaramman Malam Nafiu na kauyen gomo dake Sumaila.
Har ma kuma shugaban kungiyar ta lauyoyi bar Huwaila Muhd Ibrahim ke cewar Malam Nafiun ya daure yaron dan shekara 9 da igiya har jini ya daina gudanawa karshe yanzu hannuwansa sun kwandare sun nakasa.
You must be logged in to post a comment Login