Labarai
Ba a haifi Atiku a Najeriya ba, bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba – Malami
Atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya shaidawa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar bai cancanci ya sake tsayawa takarar shugaban kasa ba saboda ba a haifeshi a Najeriya ba.
A cewar Abubakar Malami, idan aka yi duba ga tanade-tanade da ke cikin kundin tsarin mulkin kasar nan kotun za ta amince cewa Atiku Abubakar bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba.
Ministan na shari’a ya ce kasancewa ba a haifi shi (Atiku) a Najeriya ba hakama mahaifansa saboda haka bai cika ka’idojin da sashe na 25 (1) da kuma (2) da kuma 131 (a) na kundin tsarin mulkin kasar nan.
Atoni janar na kasar ya kara shaidawa kotun cewa matukar Atiku ya tsaya takarar shugaban kasa matakin ya sabawa sashe ne 118 (1)(k) na dokokin zaben kasar nan.
Abubakar Malami y aba da wannan bahasi kan karar da wata kungiya wata mai suna MENA ta shigar gaban kotun ta bukatar kotun da ta haramtawa Atiku Abubakar tsayawa takarar shugaban kasa a babban zaben kasa da za ayi a shekarar 2023.
Ministan shari’ar ya kuma ce ko da yake dokar da ta bai wa al’ummomin arewacin Kamaru zama ‘yan Najeriya a 1961, bai bayyana cewa idan suka zama ‘yan Najeriyar daidai yake da an haife su a Najeriya ba.
You must be logged in to post a comment Login