Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba a kama Abdullahi Abbas ba – APC tsagin Ganduje

Published

on

Jam’iyyar APC tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a Kano, ta musanta raɗe-raɗin cafke shugabanta Malam Abdullahi Abbas.

Jami’in yaɗa labaranta Ahmad Aruwa shi ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio a ranar Lahadi.

Aruwa ya ce, Abdullahi Abbas da Gwamna Ganduje suna birnin tarayya Abuja domin wasu ayyuka na musamman.

Daga cikin ayyukan akwai ɗaukaka ƙarar hukuncin da kotu ta yanke kan zaɓen mazaɓun jam’iyyar a Kano.

Ya ce, “Jiya mun yi waya da shi, da safen nan ma mun yi magana, kuma nan bada jimawa ba zamu yi ƙoƙari muga mutane sun saurari muryarsa”.

Ya ci gaba da cewa, tuni suka shiga bincike kan waɗanda ke yaɗa labarin cewa an kama shugaban jam’iyyar domin ɗaukar matakin doka a kansu.

Ƙarin labarai masu alaƙa:

Mahawarar cikin jam’iyyar APC a Kano tsagin Gwamna da tsagin Shekarau

Ɗan zago ne halastaccen shugaban APC – Ɗan Sarauniya

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!