Connect with us

Labarai

PDP ta yi tir da kai wa ofishin Sanata Barau hari

Published

on

Jam’iyyar PDP reshen jihar Kano ta yi tir da harin da ƴan daba suka kai ofishin Sanata Barau Jibrin.

Hakan na cikin wani saƙon murya da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Bashir Sanata ya aike wa Freedom Radio.

A cikin saƙon Sanata ya zargi jam’iyyar APC da yunƙurin dawo da siyasar daba a Kano.

Ya ci gaba da cewa, ya kamata APC ta sani an riga an wuce irin wannan siyasar.

Ya ce “A lokacinmu mun samarwa matasa aikin yi saboda bamu yarda da irin wannan tsarinba, amma yanzu ana ƙoƙarin mayar da Kano baya”.

Ya ƙara da cewa “Matasan nan da su muke alfahari, idan ka gina su ka gina al’umma, amma idan wasu ƴan siyasa na amfani da matasa domin daba to hakan ba zai haifar mana ɗa mai ido ba”.

Labarai masu alaƙa:

Ba a kama Abdullahi Abbas ba – APC tsagin Ganduje

Mahawarar cikin jam’iyyar APC a Kano tsagin Gwamna da tsagin Shekarau

A wannan makon mai ƙarewa ne jam’iyyar APC tsagin tsohon Gwamna Malam Shekarau suka zargi ɓangaren Gwamna Abdullahi Ganduje da kai wa ofishin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau Jibrin hari.

Sai dai tsagin Gwamna Ganduje ya musanta wannan zargi.

Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta cafke wasu matasa 13 bisa zargin wannan farmaki, tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!