ilimi
Ba dalibin da zai yi jarabawa a bana sai da lambar NIN – JAMB
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta fitar da jadawalin yadda za a rubuta jarabawar neman gurbi a manyan makarantun kasar nan na wannan shekara.
A cewar JAMB za a gudanar da jarabawar neman gurbin shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) tsakanin ranakun asabar biyar ga wata zuwa asabar goma sha biyu ga watan Yunin bana.
Hukumar ta JAMB ta ce za a fara rajistar yin jarabawar ce a ranar takwas ga watan Afrilu zuwa ranar asabar goma sha biyar ga watan Mayu.
Bugu da kari hukumar ta ce ba za a kara wa’adin sayar da form na rubuta jarabawar ba.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Dr Fabian Benjamin, ta ce, an dau wannan mataki ne biyo bayan taron da shugabannin kwamitin gudanarwar hukumar su ka gudanar a ranar 22 ga watan da muke ciki na Maris.
Saboda haka sanarwar ta ce dole ne duk wanda zai yi jarabawar a bana ya kasance yana da lambar dan kasa ta (NIN)
You must be logged in to post a comment Login