Labarai
Ba don mun nema wa Maniyyata sauki ba da sai kujera ta haura miliyan 10- NAHCON

Hukumar kula da aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, ta ce, kokarin da ta yi wajen nema wa maniyyata sassaucin kudin aikin ne ya hana kowacce kujera a bana ya haura sama da naira miliyan goma.
Shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman Pakistan, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.
Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya kara da cewa ko a baya ba a samu irin wannan sassauci ba domin kowane maniyyaci ya samu ragi sosai tun daga kan na masaukai a Madina har zuwa birnin Makkah da sauran wuraren ibada da Maniyyatan bana za su ziyarta.
You must be logged in to post a comment Login