Labarai
KIRS ta rufe Makarantu da kamfanoni 7 bisa rashin biyan Haraji

Gwamnatin jihar Kano ta ce zata dauki matakin doka wajen rufe duk wani kamfani ko makarata da asibitocin da suka ki biyan haraji.
Shugaban sashin tabbatar cewa an biya harajin da Gwamnatin Kano ke bin kamfanoni da makarantu da asibitioci har ma da sauran waurare Malam Abbas Saidu, ne ya bayyana hakan bayan da suka rufe wasu kamfanoni da makarantu guda bakwai a Litinin din makon nan.
Abbas Saidu, ya kara da cewa, hukumar ta tattara haraji za ta ci gaba da bibiyar masu wuraren kasuwanci da kamfanoni don tabbatar da cewa suna biyan gwamnatin harajin da ya kamata.
Haka kuma ya kara da cewa dole ce ta sanya hukumar rufe kamfanonin sakamakon dogon lokacin da suka dauka ba tare da sauke nauyin harajin da ke kansu ba, duk kuwa da damar da hukumar ta basu.
You must be logged in to post a comment Login