Labarai
Ba mu da kudirin hana Jami’ar Sule Lamido kudin tallafi -Majalisa
Majalissar dokokin jihar Jigawa tace bata da wani kudiri na ragewa ko hana Jami’ar Sule Lamido dake Kafin Hausa kudin tallafin da kananan hukumomin jihar ke bata na kashi biyu cikin 100 daga abin da suke karba daga gwamnatin tarayya.
Shugaban kwamatin ilimi na zauran majalisar dokokin jihar Jigawa Hon. Suraja Muhd Kantoga ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda yace mutane ne suka yiwa maganar gurguwar fahimtar da ta jawo cecekuce a jihar.
Kazalika ya kara da cewa kudirin da yanzu haka ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar ba maganar cere waccan kaso da kananan hukumomin jihar suke baiwa jami’ar yake ba, illa ma kara jaddada shi, da kuma wanda ita kanta gwamnatin jihar ke baiwa jami’ar domin gudanarwa.
Haka kuma yace koda a ranar Litinin din nan da ta gabata kwamatin ilimin yayi zama da kungiyar malaman jami’ar ta Kafin Hausa, har ma da kansu suka tabbatar da cewa babu maganar hana baiwa jami’ar wancan tallafi, bayan da kwamatin ya basu kwafin kudirin suka karanta.
A ranar alhamis din ta gabata ne gwamnatin jihar Jigawa ta mika kudirin bukatar yiwa dokar jami’ar da akayi a shekarar 2013 gyaran fuska, wadda hakan ya jawo al’ummar jihar ke gunaguni, da kuma zargin a’na kokarin dena baiwa jami’ar wancan kudi ne, ya yin in da haka ta tabbata, to ba bu shakka ka iya ta’azzara tsadar kudin makaranta da daliabai ‘yan asalin jihar ke biya, k okuma ma jami’ar ta gagari ‘ya’yan masu karamin karfi.
You must be logged in to post a comment Login