Labarai
Ba mu fara sayar da takardar shiga kwalejin horas da sojoji ba – NDA
Kwalejin horas da jami’an Soji ta Najeriya NDA ta ce har yanzu bata fara sayar da takardar shiga makarantar ba karo na saba’in da uku.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwar da jami’in hulda da jama’a na kwalejin Abubakar Abdullahi ya fitar aka kuma raba ga manema labarai.
Sanarwar ta ce rahotonnin dake yawo a kafafen sada zumunta musamman na Internet cewar, yanzu haka makarantar ta fara sayar da Form din shiga kwalejin karo na saba’in da uku ba gasakiya ba ne.
Abubakar Abdullahi ta cikin sanarwar ya kuma shawarci al’umma da su yi watsi da duk wata sanarwar dake yawo cewa kwalejin ta fara sayar da form din shiga.
Ya kuma ce makarantar za ta sanar da lokacin da za ta fara sayar da form din a duk lokacin data shirya a shafinta na Internet.
You must be logged in to post a comment Login