Labarai
Ba mu muka kai ƙarar kungiyar NARD gaban kotu ba – Chris Ngige
Ministan ƙwadago da samar da samar da aikin yi Chris Ngige ya ce, ma’aikatar lafiya ta ƙasa da ofishin attorney janar ne suka shigar da ƙungiyar ƙara gaban kotu, kuma su ƙadai ne ke da hurumin janyewa.
Chris Ngige ne ya bayyana hakan, yayin zantawar sa da gidan talabijin na Channels a daidai lokacin da ƙungiyar NARD ke cika kwanaki 59 da fara yajin aiki.
Ya ce, babu abin burgewa a tafiya yajin aiki, domin kuwa zai shafi kowa da kowa ciki kuwa har da ƴan uwa da suke aiki a ƙungiyar ta NARD.
A don haka ya buƙaci ƙungiyar ta NARD da su dawo teburin sulhu don tattaunawa daga kowanne lokaci, domin kuwa gwamnati na maraba da hakan.
You must be logged in to post a comment Login