Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba muyi alkawarin mayar da N-Power din-din-din ba – FG

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce bata yi alkawarin daukan ma’aikatan wucin gadi na N-Power aikin din-din-din ba, bayan sun kammala wa’adin da ta dibar musu na shekarun biyu.

Shugaban kula da shirin samar da ayyukan jin kai na gwamnatin tarayya a jihar Jigawa, Alhaji Bala Usman Chamo ne ya bayyana hakan ta cikin shirin barka da hantsi na nan tashar Freedom Radio da ya gudana a safiyar Laraba.

Ya ce tun da fari gwamnatin ba ta yi alkawarin basu aiki bayan sun kammala aikin na wucin gadi da ta dauke su karkashin shirin N-Power ba, sai dai akwai yiwuwar hada su da babban bankin kasa don samun rancen kudaden jari da zasu gudanar da kasuwanci don dogaro da kai.

Alhaji Bala Usman Chamo ya kuma bayyana cewa kowanne wata gwamnatin na kokarin biyan ma’aikatan N-power kudaden su don tabbatar da sun yi aiki yadda yakamata tare da samun hanyoyin da za su dogara da kan su.

Ya kara da cewa, gwamnati ta kashe kimanin miliyan dari biyar don ciyar da yara abinci a gida wanda aka gudanar a jihohi hudu na kasar nan a lokacin zaman gida don tallafawa iyaye da dalibai.

Alhaji Bala Usman Chamo ya kuma ce gwamnatin tana sa ne da kudaden albashi na ma’aikatan N-Power na watannin Yuli da Yuni da ba a biya ba, hakan ya faru ne sakamakon matsin tattalin arziki da ake fuskanta sanadiyyar cutar Corona.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!