Labarai
Ba muyi nadamar zabar Buhari ba -Izala
Kungiyar jama’atu Izalatil Bidi’a Wa’ikamatissunnah mai shalkwata a Kaduna ta bayyana cewa ko kadan batayi na damar zaben shugaban kasa Malam Muhammadu Buhari ba.
Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Balalau ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Warhaka na gidan rediyon Freedom Kaduna a yau Talata.
Sheikh Balalau ya kara da cewa shugaba Buhari ya basu damar ganawa dashi, kuma sukan tattauna matsalolin da suka shafi al’umma saboda hakanne ya sanya ba’a jin su suna fitowa kafafan yada labarai kan gwamnatin ta shugaba Buhari.
Idan zaku iya tunawa dai kafin zaben shekara ta 2019 da ya gabata kungiyar Izala ta umarci dukkanin ‘ya’yan ta kan su kada kuri’ar su ga dan takarar jam’iyyar APC Muhammadu Buhari.
Zaben 2023: Ba zan sake tsayawa takara ba- Shugaba Buhari
Zaben shugaba Buhari ne yasa kungiyar IPOB ta rika cin mutuncin yan kasuwar Arewa.
Jam’iyyar APC ta sanya Aliko Dangote Femi Otedola cikin shawarwarin yakin neman zaben shugaba Buhari
Balalau ya nuna takaicin sa kan yadda wasu al’umma basa yiwa gwamnati uzri, inda ya ce a kasar nan an samu ‘yan siyasar da suke wulakanta alkur’ani saboda siyasa, sannan an samu yaron da ya hada baki aka sace shi da zummar karbar kudin fansa a wajen mahaifin sa, kuma Allah baya sauyawa mutane har sai su sun sauya.
Ga masu mummunan fata ga gwamnatin kuwa Sheikh Balalau ya ce tamkar mota ce ta dauko kowa, sai ku rika mummunan fata ga direban, kunga abin zai kara rincabewa ne ya shafi kowa da kowa.