Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Buhari ya taya shugaban kungiyar kwadago murna lashe zabe

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban gamayyar kungiyar kwadago ta kasa NLC  Ayuba Wabba murna, yayin da ya masa fatan ya kammala wa’adin sa cikin nasara, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar ba tare hamayya ba.

Har’illa yau shugaban ya taya sauran wakilan gamayyar kungiyar kwadagon Ta NLC a yayin babban taro karo na 12 da kungiyar ta yi a Abuja 

Wannan na kunshe cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar cewa shugaban kasar wanda yake neman a sake zaben sa, ya ce zai aiki tare da Ayuba Wabba, da kwamishin zartarwar kungiyar da kwamitin gudanarwar kungiyar ta kasa wanda hakan za sake karfafa dankwan dangantaka da gwamnati da kungiyar ta kwadago.

Daga cikin wadanda aka zaba ba ba tare hamayya ba,da akwai mataimakin shugaban kasa kungiyar na farko Amaechi Asuguni sai na 2 Muhammed Idris da kuma na 3 Najim Yasim.

Sauran su ne ma’ajin kudi Ibrahim Khalil sai mataimakin shugaba kungiyar na farko Abdulrafiu Adeniji sai na 2 Peter Adeyemi da na 3 Lawrence Amaechi da na 4 Oyelekan Lateef da na 5 Mercy Okezie da kuma shugaban kwamitin amintattu na kasa Adewale Adeyanju da dai sauran su.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!