Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ba ni na fara sayar da kadarorin gwamnati ba- Ganduje

Published

on

Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar, Ganduje ya yi martani ga masu korafi ko bisa sayar da kadarar gwamnati.

Gwamnan ya ce, sayar da kadarorin gwamnati ba bakon al’amari ba ne a tsarin gudanar da gwamnati.

Ganduje, ya bayana hakan ne da yammacin Alhamis din makon nan lokacin da ya ke bude sabon ginin ma’aikatar matasa da wasanni ta jihar Kano da gwamnatinsa ta gina a kusa da ma’aikatar sufuri.

Ya kara da cewa, Gwamnatin tarraya ma da kuma gwamnatin da suka yi da tsohon gwamna Engr Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso ta sayar da gidajen gwamnati ga yan siyasa da sauran jama’a.

Gwamnan, ya Kuma bukaci jami’an ma’aikatar Matasa da wasanni ta jihar Kano su yi amfani da sabbin ofisoshin da aka kaddamar din tare da kulawa da su yadda ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!