Labarai
Ba wanda zai lashe kujerar shugaban kasa a 2027 ba tare da sahalewar Arewa ba- Hakeem Baba Ahmed

Tsohon mashawarcin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan harkokin siyasa, Dakta Hakeem Baban Ahmed, ya bayyana cewa babu wani dan siyasa da zai iya lashe kujerar shugabancin Najeriya a zaben shekarar 2027 da ke tafe ba tare da goyon bayan yankin Arewa ba.
Dakta Hakeem Baba Ahmed, ya bayyana hakan ne a wata hira ta bidiyo tare da tsohon Babban Sakataren Hukumar Kula da Inshorar Lafiya NHIS, Farfesa Usman Yusuf.
Haka kuma, ya ce, nan ba da jimawa ba yankin Arewacin Najeriya zai fuskanci alƙiblarsa ta siyasa.
Dakta Hakeem Baba Ahmed, ya kuma bayyana cewa, abun da suka sani karara shi ne babu wanda zai zama shugaban kasa ba tare da goyon bayan Arewa ba.
You must be logged in to post a comment Login