Labarai
Ba za mu amince da kafofin yada labarai masu yada labaran da ke haifar da rashin tsaro – Matawalle
Gwamnatin jihar Zamfara, ta ce daga yanzu za ta fara sanya ido kan kafofin yada labaran da ke yada rahotannin game da harkokin tsaro a jihar.
Kwamishinan yada labaran jihar Malam Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a birnin Gusau, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da jami’an tsaro a jihar.
Dosara ya kara da cewa gwamnatin jihar da hukumomin tsaro za su sa ido kan rahotannin da kafofin yada labarai tare da daukar matakin da ya dace kan rahotannin da ake yadawa marasa tushe.
A cewar sa matakin ya zama dole, la’akari da yadda ake samun masu yada labaran karya ga me da sha’anin tsaro a jihar.
Dosara ya kuma ce, za a dauki mataki mai tsauri kan masu amfani da shafukan internet suna yada labaran karya.
You must be logged in to post a comment Login