Addini
Ba za mu lamunci halasta tabar wiwi a Najeriya ba – MURIC ga majalisar wakilai
Ƙungiyar da ke rajin kare martabar addinin islama ta Muslim Right Concern (MURIC), ta ja hankalin majalisar wakilai da cewa ka da ta kuskura ta halasta shan tabar wiwi a Najeriya.
Shugaban ƙungiyar farfesa Ishaq Akintola shine ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai.
Farfesa Akintola ya kuma soki batun haramta shan tabar wiwin yana mai cewa wasu gungun masu safarar miyagun kwayoyi ne ke son halasta tabar wiwin a Najeriya.
A cewar sa, a yanzu haka Najeriya tana fama da matsaloli masu yawa da suka hada da: rashin tsaro musamman rikicin boko haram da ya ki ci ya ki cinyewa ba ya ga masu satar mutane suna garkuwa da su wanda kuma kowa ya san masu aikata irin wadannan laifuka suna ta’ammali da irin wadannan miyagun kwayoyi.
Saboda haka farfesa Akintola ya shawarci mambobin majalisar da su yi watsi da kudirin.
You must be logged in to post a comment Login