Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yankin arewa zai iya haramta sana’ar sayar da kayan gyara – malami ga gwamnonin kudu

Published

on

Atoni janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami ya caccaki gwamnonin kudancin kasar nan sakamakon matakin da suka dauka na haramta kiwo a yankinsu.

A cewar Abubakar Malami haramta kiwo ga makiyaya a kudancin Najeriya dai-dai ya ke da gwamnonin arewa su haramta sana’ar  sayar da kayan gyara kasancewar al’ummar kudanci sune mafi yawa da ke gudanar da sana’ar sayar da kayan gyaran a arewa

Ministan na shari’a ya bayyana hakan ne ta cikin shirin siyasa na Politics Today a gidan talabijin na Channels.

Atoni janar na tarayyar ya bayyana matakin da gwmanonin na kudanci suka dauka da cewa haramun ne don kuwa ya sabawa doka.

A makon jiya ne bayan kammala wani taro da suka gudanar a garin Asaba na jihar Delta gwamnonin kudancin Najeriyar goma sha bakwai ta cikin wata takardar bayan taro da suka fitar suka bayyana haramta yin kiwo barkatai a yankinsu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!