Labarai
Ba za mu mara wa duk jam’iyyar da ta ki tsayar da matasa takara baya ba a 2023 – Majalisar Matasa
Majalisar matasan Najeriya ta ce ba za ta mara wa duk jam’iyyar da ta ki tsayar da matasa takara baya ba a kakar zabe mai zuwa ta shekarar 2023.
Mataimakin shugaban majalisar Abubakar Muhammad Janaral, ne ya bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi da aka tattaunawa kan muhimmacin matasa a harkokin yau da kullum.
Ya ce, kasancewar matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, don haka ba za su zuba ido a rika amfani da su ba ta hanyar da bata dace ba.
Janaral ya kuma bukaci matasa da su daina sanya kansu cikin banga siyasa, kamata yayi su mayar da hankali kan abubuwan da za su amfane su a maimakon hakan.
Ya kuma ce, bai kamata matasan zamanin nan su rika sayar da kuri’un su ba a lokutan zabe da ake basu ‘yan kudi kadan ana saye ‘yancin su.
A nata bangaren Nafisa Sulaiman mai bincike kan harkokin matasa, cewa ta yi, yanzu ya zama wajibi a rika barin matasa na shiga takara kuma a zabe su domin a rika damawa da su a sha’anin mulkin Najeriya.
Bakin biyu sun yi kira da mutane musaman matasa da suje suyi rajistar katin zabe, domin kawo sauyi a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login