Labarai
Ba zan zama shugaban ma’aikatan Tinubu ba- El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa za’a naɗa shi shugaban ma’aikatan fadar zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu.
El-rufai ya ce ‘ba zai zama shugaban ma’aikatan Tinubu ba bayan ya kammala wa’adin zangon mulkinsa na biyu a ranar 29 ga Mayun da muke ciki’.
Ganin kusancinsa da Tinubu a lokacin yakin neman zabe, rahotanni sun nuna cewa El-Rufai na cikin wadanda ake zaton za su zama shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa mai jiran gado.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login