Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina nan a kan bakana na neman kujerar shugaban majalisar dattawa- Abdul’aziz Yari

Published

on

Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma zaɓaɓɓen Sanata Abdul’aziz Abubakar Yari ‘yace yana kan bakansa kuma zai ci gaba da neman zama shugaban majalisar dattawan ƙasar nan’.

Abdul’aziz Yari, ya bayyana hakan ne jiya Asabar lokacin da yake Tattaunawa da shugabannin ƙungiyar Tinubu/Shettima Network ƙarƙashin jagorancin shugabanta Kailani Muhammad, a Abuja.

Idan za’a iya tunawa sauran masu zawarcin kujerar kamar gwamna Dave Umahi na Jihar Ebonyi da kuma Sanata Ali Ndume daga Jihar Borno sun janye tare da marawa tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom, Godswill Akpabio, wanda shi ne jam’iyyar APC ke goyon baya.

Sai dai Gwamna Yari yace duk da cewa zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya marawa Akpabio baya, hakan ba zai sa ya janye daga takararsa ba.

Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!