Labarai
Baba Impossible ya musanta fatawar da Maigida Kacako ya bayar
Wani aljani ya bayar da fatawar cewar dukan budurwa yana jawo wa aljanu su hau kanta.
Acewar Saurin har ma wannan saurayin aljani ke cewar idan iyaye suka faye dukan ‘ya’yansu mata to wannan ne ke jawo aljanu su hau kansu,
Wannan aljani mai suna Dunguzu yayi karin haske ta bakin wata budurwa da iyayen ta ke yawan dukan ta.
Dr Yakubu Maigida Kacako shine shehin malamin da yayi rukiya har wnanan aljani dunguzu ya bayyana ya kuma bayar da wnnan fatawa yayi mana karin haske akan wannan batu
To amma akan wannan batu muntaba alli,da masana a fannin aljanu da dangoginsu Dr Muhammad Tahar Adamu wanda kuma shine kwamishinan harkokin addinai na jihar kano,ya kuma bayyana cewar wannan zance gidoga ce kawai
Dr muhd Tahar adamu kenan Baba impossible.