Connect with us

Labarai

CBN ta ware biliyan 60 don sayo mitar wuta da za a rabawa jama’a kyauta

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce babban bankin ƙasa CBN ya samar da jimillar naira biliyan sittin don sayo mitar wutar lantarki, wanda za a rabawa jama’a kyauta.

 

Hakan na cikin ƙundin bayanan nasarorin da shugaba Buhari ya samu cikin shekaru shida wanda fadar shugaban ƙasa ta wallafa.

 

Ta cikin ƙundin bayanan nasarorin, gwamnati ta ce, ware naira biliyan sittin don sayo mitocin da za a rabawa jama’a kyauta na daga cikin manufofin gwamnati na daƙile matsaloli da ke addabar ɓangaren samar da wutar lantarki.

 

A cewar gwamnatin tuni aka fara shigo da irin waɗannan mitoci kuma har an samu nasarar rabawa jama’a guda dubu ɗari biyu da tamanin daga cikinsu

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!