Labarai
Babban Bankin kasa CBN ta ce batun musayar kudi tsakaninta da China ba zai hada da kayayyakin da aka haramta ba
Babban Bankin kasa CBN ya ce batun musayar kudi tsakanin Najeriya da China ba zai hada da kayayyaki 41 da gwamnatin tarayya ta haramta shigowa da su tun cikin shekarar 2015 ba.
Mukaddashin daraktan yada labaran Bankin Isaac Okoroafor ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai jiya a Abuja, inda matakin zai dakile yunkurin wasu kananan Kamfanonin kasar China wajen mayar da kasar nan tamkar jibge kayayyakinsu marasa inganci ba.
Okoroafor ya shaida cewa babban Bankin na CBN ya dauki tsauraran matakai don ganin komai ya tafi kamar yadda aka tsara.
A kwanan nan ne gwamnatin tarayya ta kulla wata yarjejeniyar musayar kudade da China ta kudi kusan Naira biliyan 720, inda kuma a ranar 23 ga watan Yunin shekarar 2015 bankin kasa CBN ya sanya takunkumin musayar kudaden domin shigo da kayayyaki daga ketare.
Wasu daga cikin Kayayyakin da aka haramta shigo da su kasar nan sun hadar da Shinkafa da Siminti da Kaji da Kifin gwangwani da kayan kitchen da Sabulai da kayan gini da dai sauransu.