Labarai
Babbar Kotun Abuja ta yi watsi da ƙorafin Nasir El-Rufai kan EFCC, ICPC da DSS

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da ƙorafin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar domin hana hukumar ICPC da sauran hukumomi rufe asusun bankinsa ko ƙwace kadarorin sa.
Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yi watsi da ƙorafin a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa ƙarar ba ta girmama kotun ba .
El-Rufai ya nemi kotun ta hana ICPC, EFCC da DSS ɗaukar matakan rufe asusunsa ko ƙwace kadarorinsa.
Ya kuma yi ikirarin cewa kuɗin sallamar da ya karɓa bayan barin kujerar gwamna tsakanin 2015 zuwa 2023 ba kuɗin haramun ba ne.
Ya nemi a biya shi diyyar Naira biliyan ɗaya da kuma Naira miliyan 100 na kuɗin shari’a.
Sai dai ICPC ta bayyana cewa El-Rufai ya raba ƙorafinsa zuwa shari’o’i daban-daban, duk da cewa suna da alaƙa da bincike guda, lamarin da ka iya haifar da hukunci masu karo da juna.
Kotun ta amince da hujjojin masu ƙara, inda ta yi watsi da ƙarar, sannan ta cire EFCC, DSS da ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya daga cikin waɗanda ake ƙara.
You must be logged in to post a comment Login