Connect with us

Labarai

Sojojin Najeria sun yi gwajin makaman cikin gida

Published

on

Rundunar Sojin Ƙasar nan  ta gudanar da gwajin sabbin kayan aikin soja da aka ƙera a cikin gida, a sansanin sojoji na Jaji da ke jihar Kaduna, daga ranar 5 zuwa 8 ga Oktoba, 2026.

A sanarwar da Laftanar Kanal Polycarp Okoye ya fitar, Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya ce bincike da ƙere-ƙeren cikin gida na taimakawa wajen inganta kayan aiki da rage dogaro da ƙasashen waje.

Shaibu, wanda Manjo Janar G. M. Mutkut ya wakilta, ya ce gwajin zai tantance inganci da dacewar kayan aikin da yanayin ayyukan soja. Ya kuma buƙaci masu tantancewa su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa da adalci domin samun sakamako sahihi.

Cibiyoyin sojoji da kamfanoni masu zaman kansu sun gabatar da kayan aiki a gwajin, yayin da aka gwada manhajojin soja a Giri, Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!