Connect with us

Labarai

ACF ta bukaci Gwamnati ta mayar da hankali kan matsalar tsaro

Published

on

Ƙungiyar tuntuba ta Arewa, ACF, ta buƙaci gwamnatin tarayya ta daina fifita kan zaɓen shekarar 2027, tare da fifita magance matsalar rashin tsaro da ke ƙara ta’azzara a ƙasar.

A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Farfesa T. A. Muhammad-Baba, ya fitar, ƙungiyar ta ce hare-hare, kashe-kashe, sace mutane da lalata dukiyoyi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke yi na barazana ga wanzuwar kasar nan. Ta zargi masu riƙe da mukaman siyasa da fifita harkokin zaɓe a kan tsaro da jin daɗin al’umma.

Kungiyar ta nuna damuwa kan ci gaba da garkuwa da mutane, tana mai cewa har yanzu ‘yan ta’adda na riƙe da yara da dama a jihohin Borno da Kwara da wasu sassan ƙasar, yayin da wasu waɗan da aka sace ke cikin mawuyacin hali.

ACF ta kuma ce an samu hare-hare daban-daban guda biyar a jihar Zamfara a rana guda, waɗanda suka yi sanadin mutuwa da sace mutane da kuma wawushe dukiyoyi. Ta ƙara da cewa ana ci gaba da samun kashe-kashe da hare-hare a jihohin Filato da Taraba, da kuma Benue da Neja da Katsina da Kogi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!