Labarai
Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin kisa ga wasu mutane biyu
Babbar kotun jiha mai lamba takwas karkashin jagorancin mai shari’a Usman na Abba ta zartar da hukuncin kisa akan mutane biyu wanda ta samu da laifin kisan kai.
Tun a shekarar dubu biyu da sha uku ne Gwamnatin jiha ta gurfanar dasu bisa zarginsu da laifin hadin baki , sata da kuma kisan kai, sai dai sun musanta zargin.
Lauyoyin gwamnati sun gabatar da shedu har guda shida, sai dai kotun bata yarda da shaidar wanda ake zargi na hudu ba inda ta sallame shi.
A cewar kotun Aliyu Abubakar da Sanin Fulani ta kamasu da laifin dumu-dumu don haka tabada umarnin a yanke musu hukuncin rataye.
Wasu gwamnatoci na yin burus da umarnin kotu- Barista Ibrahim Sule
Yau Ganduje da Abba kowa zai san matasayin sa-Kotun daukaka kara
Dole masu ruwa da tsaki su amince da hukuncin kotuna -Sarkin Kano
An kuma karawa Sanin Fulani daurin Shekaru Bakwai a gidan maza sak makon samun sa da kayan sata .
Haka kuma kotun ta ce bazata fadi ra’ayinta akan wanda ake zargi na farko ba wato Tasi’u Abudullahi kasancewar ya rasu a gidan gyaran hali.
Amma daga baya kotu tawanke Kabiru Gayawa yayin da yayi tafiyar sa.