Labarai
Babbar Kotun tarayya da ke Jihar Lagos ta mikawa gwamnatin tarayya kudaden da ta kwato daga tsohon babban Sakataren ma’aikatar kwadago da samar da aiki
Babbar Kotun tarayya da ke Jihar Lagos ta kwace kudi Naira Miliyan 664 da kuma sama da Dala 137 daga hannun tsohon babban Sakataren ma’aikatar kwadago da samar da aiki ta tarayya Clement Onubuogo, sannan ta mikawa gwamnatin tarayya.
Alkalin kotun Saliu Seidu ya bada umarnin ci gaba da tuhumar Mista Onubuogu da ake tuhuma da karkakatar da akalar kudaden shirin bada tallafi na SURE-P da gwamnatin tarayya ta yi a baya.
Lauyan Mista Onubuogu ya kalubalanci hukuncin kotun sai dai ya shaida cewa suna tattauna yiwuwar daidaitawa da EFCC a wajen Kotu, inda kuma Lauyan EFCCn Rotimi Oyedepo ya bayyana cewa tabbas suna duba yiwuwar cimma yarjejeniya a wajen kotun.
Tun a cikin watan Afrilun shekarar 2016 ne EFCC ta gurfanar da Mista Onubuogu gaban babbar kotun tarayya ta Lagos bisa zargin aikata laifuka uku ciki har da laifin kin bayyana dukiyar da ya mallaka.
Haka zalika ya gaza bada cikakkun bayanai dangane da kudi sama da Naira miliyan 93 da aka samu cikin asusunsa na Banki, ga kuma sama da Dala 139 da Fan din Ingila 10, laifukan da suka saba da sashe na 23(3)(c) na kundin hukunta laifuka na hukumar EFCC.