Labarai
Babu fashi makarantu su koma bakin aiki-Ganduje

Gwamantin jihar Kano ta ce babu fashi makarantun jihar za su koma a gobe litinin 18 ga watan Janairun 2021.
Kwamishinan ilimi na jihar Muhammad Sunusi Sa’idu Kiru ne tabbatar da hakan a Lahadin nan.
Ya ce, daga Lahadin gwamnati ta ba da umarnin bude makarantun kwana yayin da daliban jeka-ka-dawo za su koma a gobe Litinin.
A don haka ya bukaci iyaye da su yi watsi da jita-jitar da ake yadawa kan rashin komawa makarantun a gobe.
Kiru ya Kuma ce, tuni ma’aikatar ilimi ta fitar da jadawalin karatu na shekarar 2021.
You must be logged in to post a comment Login