Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

ilimi

Ganduje ya ƙara wa’adin hutun ɗalibai a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙara wa’adin mako guda kan hutun da ta bai wa daliban makarantun firamare da sakandire a faɗin jihar.

Kwamishinan ilimi na jihar Malam Muhammad Sanusu Sa’idu Ƙiru ne ya bayyana hakan, ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Malam Aliyu Yusuf ya fitar a Litinin ɗin nan.

Ya ce, ƙara wa’adin hutun, ya biyo bayan shirin daidaita jadawalin karatu, bayan da annobar corona ta sauya tsarin jadawalin da aka tsara tun da fari.

Da ɗumi-ɗumi: An rufe hanyar Kano zuwa Huguma

Sanarwar ta ce, a yanzu ɗaliban kwana za su koma makaranta a ranar Lahadi 12 ga watan Satumba mai kamawa, yayin da ɗaliban jeka-ka-dawo za su koma a ranar 13 ga watan na Satumba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!