Labarai
Babu Kasar da ke tsoma baki kan matakan da ECOWAS ke sanya wa Niger
Gwamnatin tarayya ta ce babu wata kasa dake tsoma baki dangane da matakan da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Africa ta ECOWAS ke dauka kan sojojin da suka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar.
Ministan harkokin kasashen ketare Amb. Yusuf Maitama Tuggar ne ya bayyana hakan ta cikin wani shirin talabijin na kafar yada labarai ta dailytrust, inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi kungiyar ta Ecowas da jamhuriyar Nijar.
A cewar sa ‘ko a taron da kungiyar ta gudanar a baya-bayan nan a birnin tarayya Abuja, al’amuran da suka shafi jamhuriyar Nijar din ne suka kankane tattaunawar da aka gudanar a yayin taron’.
Ministan ya kara da cewa ‘na daga cikin manufofin kafa kungiyar ECOWAS, tabbatar da wanzar da zaman lafiya da cigaban tattalin arziki da kuma tabbatar da hadin kan kasashe mambobin kungiyar’.
Rahoton: Mukhtar Abdullahi Birnin Kudu
You must be logged in to post a comment Login