Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

APC Kano: Jam’iyyar APC ta kamo hanyar wargajewa

Published

on

Wasu ƙusoshin jam’iyyar APC ciki har da sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau da Sanatan Kano ta Kudu Kabiru Gaya da kuma Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin, sun gudanar da wani taro a Abuja, inda suka yanke shawarar cewa dole ne shugabancin jam’iyyar APC na Ƙasa ya taka wa Gwamna Ganduje birki kafin lamura su dagule.

Ɗaya daga cikin ƴan jam’iyyar a Kano wanda yake cikin taron da aka yi Sha’aban Ibrahim Sharaɗa ya yiwa Freedom Radio ƙarin haske akan matakin na su.

Inda ya bayyana cewa, Jamiyyar APC ta kamo hanyar wargajewa, hakan ne yasa suka je wajen shugaban jam’iyyar APC ta ƙasa Mai Mala Buni, inda suka tattauna matsaloli da dama.

Sha’aban ya kuma ƙarƙare da cewa “muna yiwa al’umma albishir cewa, za’a ga sakamako mai kyau.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!