Labarai
Ciyo bashi don bada ilimi kyauta a Kano bai dace ba- Abdulsalam Kani
Mai sharihi kan tattalin arziki a nan Kano, ya ce, kamata yayi gwamnatin Kano ta yi amfani da kudaden asusun tallafawa harkokin ilimi, maimakon ciyo bashin naira billiyan goma sha biyar da sunan kananan hukumomi domin tallafawa shirin bada Ilimi kyauta da ta kaddamar.
Malam Abdussalam Kani na kwalejin ilimi na Sa’adatu Rimi da ke nan Kano, shine ya bada wannan shawara, ta cikin shirin Muleka mu gano na musamman na nan tashar Freedom rediyo da ya mai da hankali kan bashin da gwamnatin jihar Kano ke shirin karbowa da sunan kananan hukumomi 44 da na fadin jihar nan
Ya ce, maimakon bashin da gwamnatin ke shirin karbowa, kamata ya yi, a yi amfani da kudaden da asusun tallafawa ilimi ke bayar wa, wanda ke nuna cewa, a duk wata za a cire wani kaso daga kudaden shiga na cikin gida da jihar ke samu, sannan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi su ba da nasu kason.
Malam Abdussalam Kani ya kuma nanata cewa, matukar a naso a ciyar da bangaren Ilimi gaba, ya zama wajibi masu hannu da shuni su sanya hannu domin gwamnati kadai ba za ta iya magance matsalar Ilimi ba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdullarim Tukuntawa ya ruwaito Masanin tattalin arzikin na cewa ba da Ilimi kyauta da gwamnatin ta kaddamar, abu ne mai kyau, amma ko kadan bai dace ace gwamnati ta ciyo bashi don aiwatar da wannan shirin ba.