Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Bama wuce gona da iri a ayyukan mu – Inji Hisbah

Published

on

Hukumar Hisba ta jihar Kano ta ce babu batun wuce gona da iri a ayyukan ta kamar yadda wasu mutane ke zargi.

Babban kwamadan hukumar Muhammad Haroon Ibn Sina ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyara kasuwar Kantin kwari don yiwa yan kasuwar wa’azi.

Muhammad Haroon Ibn Sina, ya kuma ce hukumar ta Hisba na da hurumin shiga kowanne bangare a jihar Kano don duba inda ya kamata a kawar da barna.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu masu rajin kare hakkin al’umma a Najeriya su ka soki lamirin hukumar na yin aski ga matasan da ke tara suma, da kuma cafke wadanda ke lika hotunan a jikin baburan adaidata sahu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!