Labarai
Bamu Kara kudin Birkila ba – Nassi
Kungiyar masu ƙanan sana’o’i da kuma matsakaita ta jihar Kano Nassi ta musanta labarin da ake yadawa na cewar an kara kudin Burkila da kuma Lebura inda ta bayyana haka a matsayin Labaran kanzo kurge.
Shugaban kungiyar Aminu Ibrahim Kurawa ne ya bayyana haka yayin ganawa da gamayyar kungiyoyin Birkila,Lebura,Masu buga Bulo,Tifa, masu gini da kuma masu saida gidaje.
Aminu Kurawa yace wannan na zuwa sakamakon yadda wata takarda ta rinƙa yawo kan cewar an kara kudin Birkila.
Inda yace wannan kawai zance kanzo kurege ne.
Ibrahim Kurawa yace gidan bulo ne kaɗai suka kara kudin bulo sakamakon tsadar siminti.
Inci tara ya koma kan Naira dari hudu da hamsin daga Naira dari uku.
S
ai kuma inci shida da ya koma Naira dari hudu da goma da kuma hudu da ribi shima akan Naira dari hudu da goma
You must be logged in to post a comment Login