Labarai
Ban ga cin zarafin aikin jarida a diramar Labarina ba – Dakta Maude
Ƙwararren ɗan jarida anan Kano Dakta Maude Rabi’u Gwadabe ya ce, ko kusa ko alama bai ga wani cin zarafin aikin jarida da a kai a diramar Labarina ba.
“Na yi mamakin yadda mutane suke ta yin cece-ku-ce, domin kuwa na farko sun jahilci abinda ake kira da fim domin ba rahoto ba ne wani ƙirƙirarren labari ne, duk wanda ya ɗauka cewa an wulakanta ƴan jarida, yana nufin an wulaƙanta dukkanin ƴan jarida da ke cikin duniya? ko kuma na cikin kano? Idan har haka ne, to kuwa hakan na nufin cewa zargin da ake wa ƴan jarida na cewar suna ɓata gari ya tabbata”. A cewar Maude
Dan jaridar ya ci gaba da cewa “Babban abin tambaya a nan shi ne, wai shin me yasa hankalin ƴan jarida ya tashi har ma suke ta waɗannan surutan bayan ba hira akai da shi yace ga halin ƴan jaridar ba, ko don saboda Biri ya yi kama da mutum?”.
“Ƴan jarida sun yi ƙaurin suna wajen karɓar abin da ake kira “Brown Envilop” a wajan neman labarai, domin kuwa sukan sa ran za a basu wani abu, domin dayawan su basu da wata Sana’a da suka dogara da ita”. Inji Maude.
Dakta Maude ya ce, Allah ya azurta jihar Kano da yawaitar gidajen radiyo a wannan lokaci, wanda hakan ne ya sa al’umma da dama musamman masu sha’awar aikin suka shiga ciki, mafi yawa daga ciki kuma ba’a ɗauke su aiki ba suna yin aikin “sa kai” kuma babu banbanci tsakanin su da ma’aikata.
“Har yanzu a Kano an gaza magance wasu rukunin ƴan jarida da ake kira “ƴan Jandam” ta yadda suke zuwa gurare da sunan wasu gidajen Radion su naɗi murya kuma basu da inda za su je su sanya” Maude ya faɗa.
Dakta Maude ya ce, kamata yayi ƴan jarida su yiwa mashiryin fim ɗin godiya su kuma saka masa albarka a cikin abinda yayi, na fitar da wata matsala ta ƴan jaridar, wadda su kansu ƴan jaridar sun kasa magance ta.
You must be logged in to post a comment Login