Labaran Kano
Ban karbi ko sisi a hannun Magu ba – Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa, ya karbi Naira Biliyan hudu daga hannun dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, Ibrahim Magu.
Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawun mataimakin shugaban kasa, Laolu Akande ya fitar a Abuja.
Sanarwar ta ce, ofishin mataimakin shugaban kasar ya lura da yadda wani labari ke zagaya wa a shafukan sada zumunta musamman na Twitter wadda shafukan PointBlank da Newsreel suka wallafa.
Manyan laifukan da ake zargin Ibrahim Magu
EFCC:ta sake gurfanar da Babachir Lawal tare da wasu mutane uku
EFCC na bincikar Rochas Okorocha da wasu Kusoshin Gwamnati
Ta cikin sanarwar mataimakin shugaban kasar ya bayyana labarin da cewa bashi da tushe ballantana makama.
A cewar sanarwar zargin cewa Ibrahim Magu yayi almundahanar kudaden da suka kai biliyan 39 sannan ya bashi biliyan hudu a matsayin toshiyar baki shifcin gizo ne kawai.
You must be logged in to post a comment Login